Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Goodluck Jonathan ya Amince da Tsayar da shi da PDP Tayi


Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

shugaba Jonathan ne dan takara daya tilo a PDP

Shugaba Goodluck Jonathan, ya amince da tsayarda shi da jamiyarsu ta PDP, tayi, na tsayawa takara a zaben badi, koda yake, shugaba Jonathan, ne dan takara daya tilo, wakilan jamiyar, daga dukan jihohin Najeriya, su dubu biyu da dari takwas da goma sha biyu, sun kadawa Jonathan, kuri’unsu kuma ba ko kuri’a daya a cewar shugaban zaben Ken Nnamani da tayi batan kai.

Shugaba Jonathan, ya kawar da rade-radin da ake yi cewa zai jinginar da mataimakinsa, Namadi Sambo, a sabuwar takarar, inda yace shi zai sake yi masa mataimaki, da bayana shi da kuma cewa mai matukar biyayya ne.

Shugaban wanda yace zai ci gaba da yakar ta’addanci, da nuna cewa tun yakin basasa, Najeriya, bata fuskanci kalubalen tsaro kamar yanzu ba, zai dai shugaban, a wannan karon bai ambaci sunan Boko Haram, ko so daya ba, a tsawon jawabinsa na fiye da minti talatin, da ya karanta da taimakon , wasu manyan allunan karanta sakoni na nau’ra mai kwakwalwa, haka jawabin bai tabo sabbin boma-bomai, da suka fashe a Kano ba.

Shugaban jamiyar Ahmed Muazu, da shima aka tabbatar masa sahihancin shugabanci, ya kaucewa cika bakin lalle sai PDP, ta sake lashe zabe, saidai yayi adu’ar, samun nasara.

Tsohon Ministan tsaro Bello Haliru, yace koda yake bas hi zai tallata Jonathan, ba a wannan karon baya shakka da samun nasara.

Tsohon mai taimakawa shugaban kasa, ta fuskar siyasa ma Ahmed Gulak, da ya samu takarar sanata daga Adamawa, na ganin haske, a tafiyar.

Tsohon Gwamnan Zamfara, Mahmuda Shinkafi, na amsar mubayi’ar, samu tikitin takara PDP, a jihar Zamfara, zaidai shugaban jamiyar, na jihar Hassan Nasiha, yace da sauran Magana, don ba’a kamala zaben fidda gwani ba.

Shugaba Goodluck Jonathan ya Amince da Tsayar da shi da PDP Tayi - 3'56"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG