Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Jonathan Yayi Kuka Kan Rashin Zagayar Lafiya Mai Kyau


Shugaba Goodluck Jonathan
Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya baiyyana damuwar shi cewa Nijeriya tayi baya wajen maganar lafiya ta duniya baki daya.

Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya baiyyana damuwar shi cewa Nijeriya tayi baya wajen maganar lafiya ta duniya baki daya.

Yana Magana a gidan gwamnati na Abuja, yayinda yake bude taron shugabanni akan maganar zagayar lafiya ta duniya mai taken “abin hawa domin tabbataccen girma da cigaba”.

Jonathan, wanda mataimakin shugaban kasa Mohammed NamadiSambo ya wakilta, yace kasar Nijeriya ya kamata ta yi kokari ta kamo sauran kasashe, musamman wajen aiwatar da shirin lafiya na dukan kasa.

Yayinda yake baiyyana yanayin kewayar lafiya na kasa baki daya a matsayin aikin dukan kowa, yace gwamnatin tarayya, jihohi da gwamnatin kananan hukumomi hadi da kungiyoyin jama’a da kuma kungiyoyi masu zama kansu dole suyi aiki tare domin inganta bukatar cinma zagaye na lafiya cikin dukan Nijeriya.

Yace gwamnatinsa ta sa kudi sosai wajen karfafa kokarin mutane a sashin lafiya, yace kuma, “tun kayan mu sunyi kadan, dole muyi amfani da su yadda ya kamata.”

Tunda farko ministan lafiya, Prof. Christian OnyebuchiChukwu ya lura cewa a lokacin shirin wannan taro na shugabannin kasashe, anyi wata yarjejeniya cewa gwamnati dole tayi aiki da masu hannu da shuni domin ta sa aikin lafiya ya zama dole.

Bisa gare shi, idan aka aiwatar da wannan sashi na lafiya za’a sami aiyyuka a kananan hukumomi kimanin 774.

Chukwu yayi bayani cewa “yanzu da masu aiki da kuma masu taimako guda 10 kawai, aikin motar daukar marasa lafiya zata tanada aiki kimanin 77,400 kuma wannan zai kara girma a hankali zuwa miliyoyin aiyyuka.”

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG