Lahadi, Fabrairu 07, 2016 Karfe 11:23

  Labarai / Sauran Duniya

  Shugaban Amurka ya bayyana goyon bayan kwamandan kasar a Afghanistan

  John AllenJohn Allen
  x
  John Allen
  John Allen

  Kakakin fadar White Jay Carney yace shugaba Barack Obama yana ci gaba da baiwa janar John Allen cikakken goyon baya a ci gaba da aikinsa na kwamandan sojojin Amurka a Afghanistan, yayinda ake gudanarda bincike kan kwamandan bisa zargin “cudanya ko magana da  ta kaucewa ka’ida” da wata mace, wacce take tsakiyar abin fallasan nan da ya kai ga darektan hukumar CIA David Petreaus, yin murabus.

  Kakakin fadar White House din yace Mr. Obama yana ganin kimar Janar Allen da kuma irin yadda yake bautawa Amurka.

  Tunda farko shugaban Amurkan ya dakatarda zaben Janar Allen ya zama kwamandan rundunar tsaro ta NATO har  sai ma’aikatar tsaron Amurka ta kammala bincike da take yi akansa. Wata daya daya shige ne shugaban Amurkan ya zabi Janar John Allen ya zama kwamandan NATO.

  Zargin da ake yiwa janar Allen ya shafi musayar wasiku da Jill Kelly, wacce aka bayyana ta a matsayin kawa ga Petreaus da iyalinsa. Korafin da Jill Kelly ta gabatar wa hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka watau FBI, game da wasiku ta email masu barazana, daga matar da  janar Petreaus yayi lalata da  ita, itace dai matar da kuma ta rubuta littafi kan tarihin rayuwar Petreaus din, lamari da ya kai Janar din mai ritaya yin murabus daga mukaminsa na Darektan hukumar CIA.

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye