Laraba, Mayu 04, 2016 Karfe 06:59

  Labarai / Afirka

  Shugaban Kasar Misira Ya Soke Dokar Da Ya Ba Kansa Cikakken Iko

  Zanga zangar adawa da gwamnatin Mohammed Marsi
  Zanga zangar adawa da gwamnatin Mohammed Marsi
  Shugaban kasar Misira Mohammed Morsi ya soke dokar da ya kafa watan jiya, inda ya ba kansa gagarumin iko, a yunkurin shawo kan rudanin siyasa da kuma tashe tashen hankali da ake asarar rayuka da ya addabi kasar.

  Sai dai wani kakaki da ya yi magana jiya asabar da dare a Alkahira yace, za a gudanar da zaben raba gardama ranar 15 ga wannan wata na Disamba kan daftarin kundin tsarin mulkin da ake takaddama a kai.

  Kawo yanzu ‘yan hamayya basu maida martani kan soke dokar ba, babu kuma tabbacin sauyi na gaggawa da za a iya samu sakamakon  wannan sanarwar tsakanin masu zanga zanga da suka mamaye babban birnin kasar.

  Batutuwa biyu da suka hada da dokar da kuma kuri’ar raba gardaman da suka haifar da zanga zangar kin jinin Morsi, sun jijjiga kasar cikin makonni biyu da suka shige. Hadakar kungiyar hamayya da ta kunshi magoya bayan kungiyar masu sassaucin ra’ayi da wadanda basu hada harkokin addini da siyasa, ta gwamnatin da ta shude suna zargin cewa, ‘yan kishin Islama magoya bayan shugaba Morsi ne, suka rubuta kundin tsarin mulkin ba tare da hada neman gudummuwar ‘yan hamayya ba. Suna kira da  a soke kundin tsarin mulkin a shata sabo.

  Shugabannin hamayyar suna kuma zargin shugaban kasar da amfani da dokar da ya kafa ranar 22 ga watan Nuwamba wajen kafa abinda suka kira “salon mulkin kama karya na tsohon shugaba Hosni Mubarak”

  An yi sanarwa ta baya bayan nan ne bayan shafe wuni guda ana tattauna tsakanin ‘yan kishin Islama magoya bayan shugaba Morsi da kuma kungiyoyin hamayya.

  Sauti

  • Shrin Safe
   Minti 30

   Shrin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye