Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kenya Ya Bayyana Gaban Kotun Kasa da Kasa


Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta a tsakiyar lauyoyinsa
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta a tsakiyar lauyoyinsa

Lauyoyin shugaban kasar Kenya da ake zarginsa da haddasa rikicin da ya kashe mutane 1,100 bayan zaben kasarsa a shekarar 2008 sun bukaci a yi watsi da karar

Lauyoyin dake kare shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta a kotun kasa da kasa akan zargin cin zarafin dan Adam sun bukaci kotun tayi watsi da karar.

Masu gabatar da kara sun ce su basu da isasshen shaida da zasu tuhumi Mr. Kenyatta dashi.

Ana zargin shugaban ne da shirya tashin hankula bayan zaben 2008 da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 1,100.

Babban lauyan Mr. Kenyatta Steven Kay ya fadawa kotun dake zama a Hague jiya Laraba cewa ta sallameshi tare da yin watsi da karar.

Yace karar ta sukurkuce. Ta sukurkuce yadda ba za’a iya cigaba da it aba. Idan masu gabatar da kara ba zasu yi komi ba kotun ta shiga tsakani ta yi watsi da karar.

Masu gabatar da karar sun ce gwamnatin Kenya ta toshe duk hanyoyin samun takardu da suka hada da maganganun wayar tarho da na kudaden shugaban.

Ministan harkokin sharia na kasar Kenya ya fada ranar Talata cewa gwamnati tana iyakar kokarinta amma wani zubin bukatun masu gabatar da kara nada wuyan cikawa.

Mr. Kenyatta shi ne shugaban kasa na farko da zai bayyana a gaban kotun kasa da kasa.

Karar tasa ta sake jaddada sarkakiyar dake akwai wurin gurfanar da shugaban kasa da kuma samun hadin kan gwamnatinsa.

Kafin ya bayyana shugaba Kenyatta ya mikawa mataimakinsa William Ruto ragamar mulki na wani dan lokaci

XS
SM
MD
LG