Lahadi, Maris 29, 2015 Karfe 05:23

Kiwon Lafiya

Shugabannin kasashen Afirka sun jadada niyar kara hada hannu wajen shawo kan zazzabin malariya

Sauro me kawo cutar zazzabiSauro me kawo cutar zazzabi
x
Sauro me kawo cutar zazzabi
Sauro me kawo cutar zazzabi
Shugabannin kasashen nahiyar Afirka sun bayyana cewa an samu raguwar mace mace ta dalilin kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro da kimanin kashi daya bisa uku cikin shekaru goma da suka shige a nahiyar.

An bayyana haka ne a wani taron manyan kusoshin gwamnati da na cibiyoyin kasashen duniya karkashin shugabancin shugabar kasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf, wadda kuma take shugabantar kungiyar hadin kan yaki da zazzabin cizon sauro ta shugabannin kasashen Afirka (ALMA), wanda ya sami halartar wakilai da suka hada da shugabannin kasashe da shugaban hukumar hadin kan kasashen nahiyar Afirka, da wakilin babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya da kuma  sauraon manyan jami’ai.

Taron ya amince da cewa, koma bayan tattalin arziki da ake fama da shi a kasashen duniya yana kawo koma baya a kokarin cimma burin yaki da cutar a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.

Shugabannin sun kuma bayyana niyarsu ta nuna jagorancin kwarai ta waje amfani   da abinda  suke da shi a cikin gida yayinda kuma zasu ci gaba da neman hanyoyin samun tallafi daga kasashen duniya. Wannan zai taimaka wajen sa ido kan ci gaban da ake samu a yaki da cutar kanjamau da tarin fuka da kuma zazzabin cizon sauro.

A cikin jawabinsa a wajen taron, darektan yankin na Hukumar Lafiya ta duniya, Dr. Luis Sambo ya bayyana bukatar daukar kwararan matakan da zasu kai ga samun ci gaba cikin sauri a yaki da zazzabin cizon sauro da suka hada da samar da gidajen sauro da aka jika da magani masu karko da yin feshin maganin sauro gida gida da kuma amfani da matakan shawo kan cutar da aka tsara a matakin kasa da kasa.

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti