Juma'a, Yuli 03, 2015 Karfe 08:53

Najeriya

Sojoji Sun Kashe Wani Da Ake Zaton Jigon Boko Haram Ne

Sojojin sun ki bayyana sunayen mutanen, amma kakakin rundunar JTF, Leftana Iweha Ikedichi ya ce shugabanni ne a cikin kungiyar

VOA Hausa
Wani jami'in sojan Najeriya yace dakarunsu sun bindige suka kashe wani mutumin da ake kyautata zaton cewa mai magana da yawun kungiyar nan ta Jama'atu Ahlul Sunnati Lilddaawati Wal Jihad ce, wadda aka fi sani da sunan Boko Haram, sannan suka kama wasu manyan jami'an kungiyar guda biyu.

Kakakin rundunar tsaro ta hadin guiwa a Kano, Leftana Iweha Ikedichi, ya fadawa 'yan jarida cewa a yau litinin suka kai farmaki kan wani gida dake Hotoro, inda aka yi arangama da mutanen.

Kakakin ya ki ya bayyana sunan wanda aka kashe, ko wadanda aka kama, amma ya tabbatarwa da 'yan sanda cewa shugabanni ne a kungiyar ta Boko Haram.

Har yanzu ba a ji ta bakin kungiyar a kan wannan lamari na yau litinin ba.
An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: adda u musa kore balatu Daga: karamar hukumar gagarawa
18.09.2012 13:30
don Allah hukumomi kusasanta da yan boko haram domin kasanmu tazauna lafiya


by: Salisu injiniya Daga: Kano
18.09.2012 01:34
Allah ka yi mana maganin duk abin da ba zamu iya ba, ka zaunar
da kasarmu lafiya, Ameen summa
ameen.

Ra’ayoyinku da 2015 Zabe

Yaya zabe yake gudana a wajen zaben ku?

Ku sanar da mu ta Facebook, da Twitter, da Instagram @voahausa sai a kara da wannan shadar ta #zaben2015.

#zaben2015

Muna bukatar hotuna da bidiyon garin ku, ko unguwar ku, da rumfunan zaben ku, da ma duk wani abun da ya shafi zabe tsakanin APC da PDP. Ku sanar da mu ta Facebook, da Twitter, da Instagram @voahausa sai a kara da wannan shadar ta #zaben2015.

Karin Bayani akan VOA Hausa Facebook