Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta'addanci: An Cafke Mutane 16 a Brussels


Belgium Paris Attacks
Belgium Paris Attacks

Litinin cewa 'yan sanda sun damke wasu mutane 16 da ake zargin 'yan ta'adda ne a Brussels, babban birnin kasar, amma har yanzu ba a kama Salah Abdulsalam ba, mutumin da ake fi zargi dangane da kashe-kashen da aka yi a Paris

Masu gabatar da kara sun ce an raunata akalla mutum guda yayin wannan samamen.

An kaddamar da 19 daga cikin samamen ne a ciki da bayan birnin na Brusselss.

Ana kyautata zaton Abdulsalam ya ketara zuwa Belgium ranar 14 ga watan Nuwamba, 'yan sa'o'i bayan da 'yan ISIS su ka kashe mutane 130 su ka kuma raunata wasu da dama a wasu shiryayyun hare-hare a birnin Paris.

An hallaka wanda ake zargi da jagorantar hare-haren, Abdelhamid Abaaoud ranar Laraba a wani samamen da 'yan sanda su ka kai arewacin bayan birnin Paris.

Zuwa yau Litini, tasoshin jiragen kasa da makarantun Belgium sun ci gaba da kasancewa a rufe, yayin da mazauna birnin ke fuskantar rana ta uku cikin tsauraran matakai da kuma wani makon da harkokin tsaro su ka mamaye komai.

Da daddare a birnin Paris, jami'an tsaro dauke da muggan makamai, sun yi ta sintiri a titunan da akasari babu kowa ciki, yayin da birnin ke kokarin murmurewa daga kashe-kashen da ya faru.

Kafafen yada labarai a Belgium sun ce 'yan sanda sun damke wasu mutane hudu a daren ranar Asabar, daya daga cikinsu ma ana tsammanin ya yi guru da bama-baman kunar bakin wake.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG