Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kasa Ya Zama Wata Makafa ta Ambatar Ra'ayoyi


Wasu wakilan taron kasa
Wasu wakilan taron kasa

Yayin da ake cigaba da taron kasa, wasu na ganin taron ya zama wata mafakar bayyana ra'ayoyi.

Taron da yanzu yake nazari kan jawaban shugaba Jonathan yana son ya zama wata makafa ta bayyana ra'ayoyi ko muradun wakilan taron 492.

Kamar wakili daga Rivers, Samuel Agaku, yana bukatar a bi tsarin mulkin tarayyar Najeriya inda shi a gareshi kowane sashi ya mallaki arzikinsa kacokan. Kalamun nasa sun biyo bayan watsi da makalewa man fetur daga 'yan arewa. Su 'yan arewa sun nuna arzikin noma shine dahir.

Wakili daga jihar Borno Dr. Yerima Shettima yace "kada talakawa su yi tsammanin wani abu wanda zai share masu hawaye zai fito daga taron." Yace su sake yin tunani domin taron bashi da wata doka da ta bashi iko ko karfi kamar majalisun kasa. Ya kara da cewa "komenene aka tattauna a taron sai ya je majalisa."

To amma tsohon ministan 'yan sanda, Adamu Maina Waziri, yana da kwarin gwiwa kan taron. Yace taro ne wanda ya kunshi mutane daban-daban. Najeriya kuma ta kunshi mutane daban-daban da addinai daban-daban. Mutanen Najeriya kuma suna da akidu daban-daban. Saboda haka duk wani rudani da matsala suna nan cikin taron. Yace sun riga sun tafasa cikin kwanaki biyu da suka fara taron. Yanzu sun huce kuma yana fata "cikin ikon Allah Zai cigaba da sasu cikin natsuwa su yi abun da zai zama alheri ga kasar."

Shugaban kungiyar kananan hukumomi, Ibrahim Khalil, ya samu magoya baya da dama a taron, wajen samarwa kananan hukumomin Najeriya 774 'yancin cin gashin kansu.

Ga rahoton karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG