Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UNICEF da Zamfara na yaki da Gubar Dalma


Ma'aikatan kiyon lafiya ne a nan suke aikin share wani gida don raba shi da dattin gubar dalmar da ta mamaye shi a kauyen Dareta dake Gusau, Nigeria.
Ma'aikatan kiyon lafiya ne a nan suke aikin share wani gida don raba shi da dattin gubar dalmar da ta mamaye shi a kauyen Dareta dake Gusau, Nigeria.

Kungiyar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta shirya taron karawa juna ilmi na kwannaki biyu a Gusau, hedkwatar jihar Zamfara, inda gubar dalma ta kashe mutane da dama masu aikin hakar zinari. Sani Abdullahi Tsafe na dauke da rahoto daga Gusau.

Cibiyar kula da kananan yara ta Majalisar dinkin duniya (MDD) ta shirya taron kwannaki biyu na karawa juna ilmi kana saran rayukkan da ake fama da ita a wajen aiyukkan hakar ma’adinai a nan jihar Zamfara. Jami’in kiyon lafiya na jihar zamfara Alhaji Aminu Idris yace shirya irin wannan taron ya zama wajibi sabnoda yawan rayukkan da ake rasawa a cikin aikin. Sarakuna jihar Zamfara 17 da uwayen kasa da hakimmai sun halarci wannan taron, kuma wasunsu, kamar Tekun Nahuce, sun bayyana cewa taron yana da anfani. Suma shugabannin kanan hukumomi an gayyato su. Shugaban karamar hukumar mulkin Zurmi, Alhaji Garba Dauran, shima ya bayyana fatar shirin zai anfani jama’a. Ya kuma yi fatar sarakuna da iyayen kasa zasu wayarda kan jama’a kan hatsarin dake tattare a cikin aikin hakar ginar zinari.

XS
SM
MD
LG