Talata, Satumba 16, 2014 Karfe 02:54

Sauran Duniya

Manyan Jiragen Ruwa Biyu Sun Yi Karo a Teku Dake Gabashin Ingila.

Wasu jiragen dakon kaya, a babbar tashar jiragen ruwa dake Los Angeles, jihar California.Wasu jiragen dakon kaya, a babbar tashar jiragen ruwa dake Los Angeles, jihar California.
x
Wasu jiragen dakon kaya, a babbar tashar jiragen ruwa dake Los Angeles, jihar California.
Wasu jiragen dakon kaya, a babbar tashar jiragen ruwa dake Los Angeles, jihar California.
Laraba masu aikin ceto sun tsamo gawarwaki mutane uku daga cikin teku dake arewacin Ingila, kuma suna neman wasu ma’aikatan jirgin ruwa na dakon kaya su takwas, wadanda jirgin da suke aiki ciki  ya nutse dab da gabar ruwan kasar Netherlands, bayanda ya yi karo da wani jirgin ruwa, shi ma na dakon kaya.

A aikin ceton da ake gudanarwa, dogarawan ruwa Dutch sun yi amfani da jirage masu saukar ungulu wajen ceto ma’aikata 13 daga jirgin daukar kayan mai suna Baltic Ace.

Jirgin ruwan wanda yake dauke da tutar kasa r Bahamas yana da ma’aikata 24, ya nutse ne bayan da wani jirgin dakon kaya mai suna Corvus J ya kara masa , a wani bangare na tekun inda ake yawan zirga zirgan jirage, da tazarara kilomita 50 daga tashar jiragen ruwa dake Rotterdam.

Har dai a daren jiyan, jirgin dakon kaya Corvus J, mai dauke da tutar Cyprus yana kan ruwa, kuma babu alamar yana fusknatar hadarin  nutsewa.

Har a zuwa daren jiya masu aikin ceto sun gayawa manema labarai cewa suna ci gaba da neman ko watakil a sami wani da rai. Koda yake suka ce bayan sa’ao’I hudu da hadarin zai yi wuya a sami mutum da rai cikin ruwan kankara zai yi wuya.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Rediyo/Sauti

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +1-202-619-0548 ko kuma +1-202-619-0551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +1-202-205-9942.
 

Audio Shirin Safe     Rumbun Shiri    Live

           0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi  Rumbun Shiri   Live

           0700 - 0730 UTC 

Audio Shirin Rana     Rumbun Shiri   Live

            1500 - 1530 UTC 

Audio Shirin Dare     Rumbun Shiri   Live

            2030 - 2100 UTC