Asabar, Nuwamba 28, 2015 Karfe 01:26

Labarai / Sauran Duniya

Wani Shirgegen Dutse Daga Sarararin Samaniya Ya Dira A Rasha.

Hoto wani dutse da na'urorin hukumar NASA ta Amurka ta dauka.Hoto wani dutse da na'urorin hukumar NASA ta Amurka ta dauka.
x
Hoto wani dutse da na'urorin hukumar NASA ta Amurka ta dauka.
Hoto wani dutse da na'urorin hukumar NASA ta Amurka ta dauka.
Aliyu Imam
Jami’an kasar Russia sun ce wani shirgegen dutse ya fado daga sararin subahana ya dira a sassan duwatsun Ural da ke Russia yau jumma’a,  wanda ya sa wuta ta kama kuma gilassan tagogi suka farfashe.

Jami’an sun kara da cewa mutane fiye da 400 ne suka raunata a yankin Chelyabinsk, yawancin su sun sami rauni da gilassan da suka farfashe.

Jami’an karamar hukuma sun ce bango da soron  masana’aantar Chelyabinsk sun lalace a sanadiyar fadowar dutsen.

Hukumomi kuma sun ce wayoyin sadarwa na- tafi- da gidan ka, suna nan suna aiki.

Shirgegen dutsen ya fado ne yan sa’o’i kadan kafin wani karon da aka hasashe zai auku tsakanin wata tauraruwa mai suna 2012 DA14 da duniyar mu. Hukumar binciken yanayin sararin samaniya Amurka da ake kira NASA, tace, wannan tauraruwa mai kimanin fadin mita 45 zata iya zuwa kusa da duniyar mu da kimanin kilomita 27,000 daga sararin samaniya.

Hukumar ta jaddada cewa taurauwar ba zata fado duniyar mu ba.

A dandalin twitter na internet, hukumar binciken yanayin sararin samaniya ta Turai ta ce shirgegen dutsen da ya fado a yankin Rasha daga saman yau jumma’a, ba shi da wata alaka da tauraruwar.

Sauti

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye