Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jos: Fashewar Tukunyar Gas Ta Chlorine A Ta Halaka Akalla Mutane 8, Wasu Fiye Da 100 Suna Asibiti..


Macedonia, fashewar iskar Gas.
Macedonia, fashewar iskar Gas.

Tukunyar sinadarin "Chlorine" din na matatar ruwa dake birnin na Jos ne.

An sami fashewar tukunya da ake adana sinadarin "Chlorine", wadda hukumar samar da ruwa a yankin Jos, take amfani da shi wajen tace ruwa. Da asubahin Asabar din nan ne al'amarin ya auku wadda ya janyo halakar mutane akalla takwas, wasu fiye da dari kuma aka kai su asibiti domin jinya.

Tukunyar da ake adana sinadarin "Chlorine" din da ake amfani da shi wajen tsabtace ruwan sha a matatar ruwa da ake kira Lamingo yayi bindiga, sinadarin da ya zama iska kuma aka shaka, yana kisa, ko illa sosai.

Hukumomi a jihar Flaton, sun tabbatar da aukuwar lamarin, kuma tuni kakakin gwamnatin jihar, Emmanuel Nanle, yace Gwamnan jihar Simon Lalong, ya bada umarnin a sauya dukkan kayan aiki a matatar ruwan da suka tsufa.

Wakiliyar Sashen Hausa Zainab Babaji, ta ziyarci asibiti inda galibin wadanda suka jikkata suke karbar jinya, tace wadansu daga cikinsu, an saka musu bututun shakar iska.

Amma wadanda rauninsu baiyi tsanani ba sun yi bayanin yadda lamarin ya auku.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG