Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar WikiLeaks Ta Sake Bayanan Sirrin Amurka Dake Zargin Shugaba Omar al-Bashir Na Sudan Da Satar Dala Milyan Dubu Tara( $9)


Shugaban kungiyar Wikileaks,Julian Assagne,yake magana da manemalabarai a harabar kotu da ta bada belinsa,ranar Alahmis.
Shugaban kungiyar Wikileaks,Julian Assagne,yake magana da manemalabarai a harabar kotu da ta bada belinsa,ranar Alahmis.

Bayanan da Jaridar Guardian ta Ingila buga yana cewa babban mai gabatar da kara agaban kotu kasa da kasa Luis Moreno-Ocampo,yana gayawa jami'an jakadancin Amurka cewa farin jinin al-Bashir zai zube da zarar jama'a suka game cewa ya wawuri dukiya mai yawa ya boye.

Kungiyar Wikileaks ta saki bayanan sirrin kafofin difilomasiyyar Amurka da suka nuna cewa shugban Sudan Omar al-Bashir ya saci dala milyan dubu tara daga kudaden man kasar.

Bayanan sirrin da jaridar Guardian ta buga yace babban mai gabatar da kara a gaban kotun kasa da kasa Luis Omreno Ocampo,ya gayawa jami’an difilomasiyyar Amurka cewa al-Bashir ya boye kudaden a wani asusunsa dake bankin Lyods na Ingila.

Bayanan sun nuna Mr.Ocampo,wanda tuni yake farauntar Mr. Bashir kan laifuffukan yaki, yana cewa farin jinin Mr.Bashir zai zube da zarar jama’a sun fahimci irin yawar dukiya da ya boye.

Shi dai Mr. Bashir bai fito fili ya yi magana kan wan nan zargi ba,amma wasu manyan kusoshin gwamnatinsa biyu sun fito sun ce,kalaman Mr. Ocampo ba gaskiya bace.

XS
SM
MD
LG