Alhamis, Yuli 02, 2015 Karfe 17:32

Afirka

'Yan Fashi A Jamhuriyar Benin Sun Afkawa makabarta

Shugaba Thomas Boni Yayi, na Benin wanda kuma har wayau shine shugaban kungiyar kasashen Afikra. Shugaba Thomas Boni Yayi, na Benin wanda kuma har wayau shine shugaban kungiyar kasashen Afikra.
x
Shugaba Thomas Boni Yayi, na Benin wanda kuma har wayau shine shugaban kungiyar kasashen Afikra.
Shugaba Thomas Boni Yayi, na Benin wanda kuma har wayau shine shugaban kungiyar kasashen Afikra.
A Benin ‘yan fashi sun tone kaburbura fiye da dari a wata makabatara dake kusa  Porto-Novo babban birnin kasar, a wasu lokutan suna yanke wasu sassan na jikin gawarwakin.

Hukumomin kasar sun fara binciken sace sacen ne a a wani kauye da  ake kira Dongbo, bayan da wani birkila da  yake aiki a makabartan ya tuntubi ‘Yan sanda.

A hira da Muriyar Amurka ranar  jumma’a, wani wakilin a tashar talabijin a Benin Charlot Ogou, yace barayin sun yanke kawunan wasu gawarwakin. Yace wannan shine karo na farko cikin shekaru biyar da aka aikata irin wannan satar.

Wakilin yace ‘Yan sanda basun tantance dalilin satar ba, kuma sun ki suce ko sace sacen gawarwakin yana da nasaba da tsafe-tsafe da  ya tsananta. Wannan lamari yana da karfi sosai a kasar.

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti