Lahadi, Mayu 01, 2016 Karfe 12:45

  Labarai / Sauran Duniya

  Dubban 'Yan Hamayya Suna Zanga Zanga A Masar

  Masu zanga zanga a dandalin Tahrir suke gudu daga hayaki mai sa hawaye da 'yan sandan kwantarda tarzoma suka harba.Masu zanga zanga a dandalin Tahrir suke gudu daga hayaki mai sa hawaye da 'yan sandan kwantarda tarzoma suka harba.
  x
  Masu zanga zanga a dandalin Tahrir suke gudu daga hayaki mai sa hawaye da 'yan sandan kwantarda tarzoma suka harba.
  Masu zanga zanga a dandalin Tahrir suke gudu daga hayaki mai sa hawaye da 'yan sandan kwantarda tarzoma suka harba.
  A Masar masu zanga zanga a birane kasar masu yawa, sun kai hari kan ofisoshin  kungiyar “Ya ku ‘Yan uwa musulmi”, ko Muslim Brtoherhood a turance, a yayinda ‘yan hamayya da kuma masu goyon bayan gwamnati, suka yi zanga zanga a binrin alkahira, kan wata sabuwar  dokar da shugaban kasar ya kafa.
  Magoya bayan shuga Morsi suke zanga zanga da kirari yayinda suke maci.Magoya bayan shuga Morsi suke zanga zanga da kirari yayinda suke maci.
  x
  Magoya bayan shuga Morsi suke zanga zanga da kirari yayinda suke maci.
  Magoya bayan shuga Morsi suke zanga zanga da kirari yayinda suke maci.

  Tarzomar ta zo ne kwana daya bayan da shugaba Mohammed Morsi, ya fifita kansa daga kan ko wani bangare na mulki, tare da ayyana cewa babu wata kotu ko hukumar kasar da take da  ikon ta kalubalanci duk  wata shawara da  ya yanke. 

  A cikin wani jawabi da ya yiwa magoya bayansa a fadar shugaban kasa jiya jumma’a, Mr. Morsi yace burinsa shine  ganin Masar ta kasance kasa dake da kwanciyar hankali da  kuma zata samu ci gaba cikin tsanaki, kuma bashi da niyyar zama  mai cikakken iko kan ko wani lamari na kasar.

  Dubban magoya bayan ‘yan hamayya ciki harda mai ra’ayin ‘yan baruwana Mohammed ElBradei, wanda shine tsohon  shugaban hukumar hana yaduwar makaman Atomic na Majalisar Dinkin Duniya, sun hallara a dandalin Tahrir jiya jumma’a, domin zanga zanga kan shawarar da shugaban kasar ya yanke, yayinda ‘Yan Sanda suka harba bornon tsohuwa kan gungun masu zanga-zangan. 
  ElBaradei ya zargi shugaban kasan da  cewa ya zama “sabon fir’auna” domin ya ayyana kansa a zaman shugaba mai dumbin iko.

  A biranen Port Sa’id, da Isma’ila, da  Alexandria, anga masu zanga zanga suna jifa  da duwatsu da wasu abubuwa msu fashewa, da kuma cunna wuta kan ofishin  kungiyar Muslim Bortherhood mai mulkin kasar.

  Watakila Za A So…

  Obama Ya Halarci Taron Cin Abincin Dare Na Karshe Na KUngiyar 'Yan Jarida

  Wannan shine karo na takwas kuma na karshe da 'yan jarida masu aiki a fadar white suka a zamanin mulkin Obama Karin Bayani

  Za'a Iya Dasa Kan-Dan-Adam Kan Wata Gangar Jiki?

  Wasu likitoci suka ce wannan hauka ne kawai, kuma ba zai yi aiki ba. Karin Bayani

  Zika Ta Kashe Mutum Na Farko A Amurka.

  Mutumin dan shekaru 70 da haifuwa a watan febwairu ne ya kamu d a cutar da Zika. Karin Bayani

  A Kenya Wani Gini Mai Hawa 7 Ya Fadi Da Mutane A Ciki.

  Ambaliyar ruwa ne ya janyo faduwar ginin dake wata unguwar marasa galihu. Karin Bayani

  Sauti Najeriya Ba Zata Kara Kashe Kudi Ba Don Nemawa Jami’anta Magani A Kasar Waje

  Duk da yake kowanne dan kasa na da ‘yancin fita domin neman waraka daga cutar dake damunsa, babban abin takaici inji shugaban Najeriya Mohammadu Buhari, a ta bakin ministan lafiya, shine yadda yan kasar ke yin tururuwa a kasashen waje domin neman maganin rashin lafiya. Karin Bayani

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye