Talata, Disamba 01, 2015 Karfe 03:04

Labarai / Najeriya

'Yan Najeriya Da Nijar Zasu Ga Khusufin Rana

Ran Lahadi 3 Nuwamba, 2013 tun daga misalin Karfe 1:15pm na azahar za a fara ganin Khusufin Rana a fadin Najeriya da Nijar da sauran kasashen Afirka

Yadda mutane a wasu sassan kasar Gabon zasu ga husufin ke nan, amma a Najeriya da Nijar, wata zai tare gefen rana ne kawai ba zai rufe ta gaba daya ba.
Yadda mutane a wasu sassan kasar Gabon zasu ga husufin ke nan, amma a Najeriya da Nijar, wata zai tare gefen rana ne kawai ba zai rufe ta gaba daya ba.
Idan Allah Ya kai mu ranar lahadi 3 ga watan Nuwamba, 2013 a bana, akwai gagarumin husufin rana da zai wakana da azahar, agogon Najeriya, wanda kuma za a iya ganinsa na lokaci mai tsawo a Najeriya da Nijar da sauran kasashen Afirka.

Wannan daya ne kawai daga cikin abubuwa na ban mamaki da zasu wakana a sararin samaniyar wannan bangare namu na duniya a shekarar nan domin kuwa a cikin watan Disamba, za a fara ganin wata babbar bakuwar, watau tauraruwa Mai Wutsiya da aka sanya ma suna "Comet Ison" wadda zata yi watanni ana ganinta daga doron duniyar bil Adama, safe da kuma dare, kafin ta wuce can cikin sararin subhana nesa da Ranar bil duniyar bil Adama.

Khusufin Rana da za a yi Lahadi 3 Nuwamba, zai fara daga karfe 11:05 agogon Najeriya a yankunan da suke gabashin Amurka, kuma zai bi ta kan tekun Atlantika zuwa Afirka har ya wuce zuwa Madagascar da gabas ta Tsakiya. Wuri na karshe da zai ga khusufin nan zai wakana da karfe 4:28 na la'asar agogon Najeriya a kuryar gabashin Afirka.

Mutanen da suke dukkan kudancin Turai da kudancin Amurka ma zasu ga wani bangare na wannan khusufin, amma wurin da za a fi ganinsa baki daya, shi ne inda zai fara hawa doron kasa a yammacin kasar Gabon da misalin 2:45 na azahar agogon Najeriya.

A Najeriya, za a fara ganin wannan khusufin ranar a lokuta dabam-dabam na ranar lahadi 3 Nuwamba, amma duk bambancin na 'yan mintoci ne. Alal ga misali, ga wanda yake zaune a garin Bauchi a Jihar Bauchi, za a fara ganin Khusufin Ranar da misalin karfe 1:10 na azahar. Khusufin zai kai makura daga nan Bauchi da karfe 2:44 na azahar, sannan zai gama bacewa baki daya da karfe 4:05 na la'asar. (Mai son sanin lokutan da za a fara gani, ko za a fi gani, ko za gama gani a garinsu, yana iya karawa ko rage 'yan mintoci cikin wannan lissafi, ko kuma ya tuntube mu don neman cikakken bayani).


(Taswirar dake nuna wuraren da zasu ga khusufin rana da kuma lokutan ganin haka a agogon UTC)

Khusufin Rana yana faruwa a duk lokacin da wata ya shige ta tsakanin duniya da rana, a daidai lokacin kamawar sabon wata. Akwai khusufi kala uku: mai gaba daya, da wanda ke kama gefe, da kuma wanda ke sanya ganin inuwa kawai, amma ba ya rufe ranar.

Khusufin wata kuma, yana faruwa idan duniya ta shiga tsakanin rana da wata a lokacin da wata yake cike a sama, watau dai da misalin tsakiyar kamawar wata.

Ana iya gano lokutan da Khusufi na Rana ko na Wata zai faru ne a saboda ana iya auna saurin juyawar duniya da wata da yadda suke kewaya rana.

HATTARA: A yi hattara sosai wajen kallon Khusufi, domin kallon rana da idanu haka kawai ba tare da tabaro baki sosai ba, zai iya makanta mutum. A tabbatar sai rana ta gama rufewa baki daya kafin a ce za a kalle ta

Idan ana neman karin bayani, ana iya aiko mana da sako ta email (iahmed@VOANews.com)

Watakila Za A So…

Shirin Dare

Shirin Dare

A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.
Yau da Gobe

Yau da Gobe

Yau da Gobe shiri ne mai inganta rayuwar matasa cikin fadakarwa da ilmantarwa da kayatarwa, ya kuma karfafa mu su samun kaifin fahimtar matsalolin da suka addabe su, suka dabaibaiye su a wannan zamani. Shirin Yau da Gobe na zuwa sau biyar a mako, Litinin zuwa Jumma’a, daga karfe 4 da rabi na yamma zuwa karfe 5! Yau da Gobe ya hada komai, daga filin dafe-dafen gargajiya, zuwa zauren matasa inda suke bayyana ra’ayoyin su daban-daban akan wasanni, da siyasa, da mu’amala ta samari da ‘yan mata, da fasaha, da filin kiwon lafiyar matasa.
Shirin Rana

Shirin Rana

Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.
Shirin Hantsi

Shirin Hantsi

Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
Shrin Safe

Shrin Safe

Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.

An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Sauti

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe shiri ne mai inganta rayuwar matasa cikin fadakarwa da ilmantarwa da...

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shrin Safe
  Minti 30

  Shrin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye