Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Siyasar Ukraine Basa Yi Da 'Yan Aware


​Mutumin da ake kyautata zaton shi zai zama zababben Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya ce ba babu wani zancan tattaunawa da wadanda ya kira "'yan ta'adda" wanda wannan shi ne yadda ya kan bayyana 'yan aware magoya bayan Rasha masu dauke da makami.

Poroshenko ya fadi jiya Litini cewa za a cimma zaman lafiya ne ta wajen tattaunawa da wadanda ya kira "mutane" kuma makamai ne kadai za a yi amfani da su wajen tinkarar wadanda ya kira makasa.

Ya kuma ce ya na so a shiga tattaunawa da Rasha, wanda hakan ya dadadawa Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergie Lavrov, wanda ya ce bai kamata a salwantar da duk wata damar tattaunawa da Ukraine ba.

Shugaban 'yan tawayen Ukraine a Donetsk shi ma ya ce a shirye ya ke ya tattauna da Poroshenko, to amma sai idan tattaunawar za ta ta'allaka ne kan musayar fursunoni da kuma janyewar sojojin Ukraine daga gabashin kasar.

A halin da ake ciki kuma, ba a iya tabbatar da ko waye ke rike da filin jirgin saman Donetsk, bayan da 'yan tawayen su ka kwace wani sashinsa a jiya Litini, wanda hakan ya janyo harin jirgin sama daga gwamnatin Ukraine.

Sakamakon da ba na hukuma ba ya nuna cewa hamshakin attajirin nan mai kamfanin kayan lashe-lashe dangin candy Poroshenko shi ya ci zaben Shugaban kasar da gagarumin rinjaye.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Johan John Kerri ya ce fitowa da yawa da masu kada kuri'a su ka yi ya nuna cewa mutanen Ukraine na son zama bisa turbar dimokaradiyya ta salon Turai.
XS
SM
MD
LG