Jumma’a, Mayu 06, 2016 Karfe 15:54

  Labarai / Sauran Duniya

  Shugaba Obama Da Mr. Romney Sun Yi Yakin Neman Zabensu Na Karshe.

  Mr. Romney da shugaba Obama a muhawararsu ta karshe.Mr. Romney da shugaba Obama a muhawararsu ta karshe.
  x
  Mr. Romney da shugaba Obama a muhawararsu ta karshe.
  Mr. Romney da shugaba Obama a muhawararsu ta karshe.
  Aliyu Imam
  A jajiberen babban zabe a nan Amurka, shugaba Barack Obama na Amurka da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican dake kalubalantarsa, Mitt Romney, sun yi yakin neman zabe na karshe a muhimman jihohin da sune zasu iya shata wanda zai lashe wannan zabe na yau talata, wanda har yanzu babu wanda yayi ma wani fintinkau a cikinsu.

  A Jihar Wisconsin, shugaba Obama ya zargi Mr. Romney da kokarin yin ado ma munanan manufofin da ‘yan Republican suka aiwatar a can baya, yana mai cewa kasar nan ba zata samu nasara ba har sai ta bunkasa al’ummar dake tsaka tsaki

  Zamu ci gaba da gwagwarmayarmu a saboda mun san Amurka a koda yaushe tana bunkasa. Muna samun gawurta a duk lokacin da aka ba kowa dama, a duk lokacin da kowa ya dafa daidai wa daida, kuma a duk lokacin da kowa ke aiki da ka’idoji iri daya.

  Abinda muka yi imani ke nan. Wannan shi yasa kuka zabe ni a 2008, kuma wannan shi ne dalilin da yasa nake neman wa’adi na biyu a matsayin shugaban Amurka.
  A wajen wani gangamin da yayi da sanyin safiyar jiya a Jihar Florida, Mr. Romney ya fadawa magoya bayansa cewa shugaban dan jam’iyyar Democrat, ya kasa cika alkawuran da yayi har ya ci zaben 2008.

  Shugaban nan yayi alkawarin kawo canje-canje masu yawa, amma ai ba iya jawabi ne canji ba. Ana auna canji ne ta hanyar nasarorin da mutum zai gani a kasa. Shekaru hudu da suka shige, Obama yayi alkawura da yawa lokacin da yake takara, amma kuma kash, har yanzu ya kasa cimma su.

  Masu fashin bakin siyasa a nan Amurka suka ce daga cikin jihohi guda hamsin na Amurka, ‘yan kalilan ne kawai zasu iya fayyace wanda zai ci zaben na yau talata, a saboda akasarinsu an riga an san ko dai shugaba Obama ko Mr. Romney ne zasu lashe su. ‘Yan jihohin da har yanzu ba a san wanda zai lashe su ba, sune ake yakin neman zabe kansu gadan gadan. Zaben shugaban kasa na Amurka, ba wai ana yinsa ne ta kirga illahirin kuri’un da aka kada domin ganin mai rinjaye ba, ana yinsa ne bisa tsarin zaben wakilai ko mazaba wadanda sune a zahiri zasu zabi shugaban kasa. Yawan wakilai ko mazaba na kowace jiha, ya danganci yawan jama’arta idan an kwatanta da sauran jihohin kasa.

  A bayan gangamin da yayi a Wisconsin, shugaba Obama ya yada zango a Jihar Ohio, kafin ya zarce zuwa Jihar Iowa, inda a yanzu haka yake gudanar da yakin neman zabensa na karshe. Mr. Romney ya yada zango a Ohio da Jihar Virginia, sannan ya zarce zuwa Jihar New Hampshire.
  Miliyoyin jama’a a kasar nan dai sun riga sun kada kuri’unsu karkashin dokokin jefa kuri’a da wuri a wasu jihohi. Amma mafi yawan masu jefa kuri’a yau ne zasu doshi rumfunan zabe da za a kakkafa a makarantu da gidajen ‘yan kwana-kwana da coci-coci.

  Kuri’un neman ra’ayoyin jama’a dabam-dabam sun nuna ‘yan takarar biyu su na kunnen doki a kasa. Amma a kuri’un neman ra’ayoyin masu jefa kuri’a a jihohi guda 9 wadanda sune zasu tantance wanda zai lashe wannan zabe, sun nuna shugaba Obama yana kan gaba a akasarinsu, amma da ‘yar rata kadan. Romney yana kan gaba a cikin jiha kwaya daya tak ne daga cikin wadannan jihohi, watau a Jihar Florida.

  Watakila Za A So…

  Harin Syria kan sansanin yan gudun hijira ya kashe mutane 30

  Sa'o'i kadan bayan jami'an Rasha da Syria sun tabbatar da tsagaita wuta a birnin Aleppo sai jiragen yaki na Syria ko Rasha suka soma ruwan bamabamai kimanin kilimita 30 daga birnin lamarin da ya kaiga hasarar rayuka 30 Karin Bayani

  Sauti Shugaba Umaru Musa Yar'adua ya jagoranci Najeriya bilhaki da gaskiya - Jonathan

  Shekaru shida ke nan da Allah ya yiwa tsohon shugaban Najeriya Umaru Musa Yar'adua rasuwa, rasuwar da ta kaiga mataimakinsa Goodluck Jonathan daga yankin Niger Delta ya dare kan mulki Karin Bayani

  Wasu mayakan sa kai sun farma kamfanin hakan man fetur na Chevron a Niger Delta

  Rundunar sojojin ruwan Najeriya ko Navy ta sanar jiyar Alhamis cewa wasu mayakan sa kai sun farma kamfanin hakan man fetur na Chevron a matsayin wani hari na baya bayan nan da suka aiwatar a yankin Niger Delta Karin Bayani

  Kakakin Majalisar Wakilan Amurka yace ba zai iya goyon bayan Trump ba

  Kodayake hamshakin attajirin nan Donald Trump shi kadai ne dan takarar shugabancin Amurka daga jam'iyyar Republican ya rage, kakakin majalisar wakilan Amurka shi ma dan jam'iyyar Republican yace ba zai iya goyon bayan attajirin ba. Karin Bayani

  Sauti Rundunar sojojin Najeriya ta samu nasarar kubuto wasu mutane a dajin Sambisa

  A cigaba da yakin da sojojin Najeriya keyi da 'yan ta'adan Boko Haram, rundunar soji ta bakawai dake Maiduguri ta samu nasarar kubuto wasu mutane da dama daga dajin Sambisa Karin Bayani

  Sauti Majalisar dokokin Nijar ta amince a ciwo bashi domin inganta wutar lantarki a karkara

  A karkashin dokokin da majalisar ta amince dasu kimanin biliyan goma sha shida na kudaden sefa ne gwamnatin ta Nijar zata ranto daga bankin cigaban Afirka ta yamma domin inganta wutar lantarki a yankunan karkarar kasar Karin Bayani

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye