Jumma’a, Maris 27, 2015 Karfe 20:04

Afirka

'Yan Sanda a Kenya Sun kashe Mutane Biyu Da Ake Zargi 'Yan al-Shabab Ne.

Bindigogi da albarusai da 'Yansanda suka gano a wani lamari na daban, har suka kama mutane biyu da ake zargi suna da alaka da al-Shabab.Bindigogi da albarusai da 'Yansanda suka gano a wani lamari na daban, har suka kama mutane biyu da ake zargi suna da alaka da al-Shabab.
x
Bindigogi da albarusai da 'Yansanda suka gano a wani lamari na daban, har suka kama mutane biyu da ake zargi suna da alaka da al-Shabab.
Bindigogi da albarusai da 'Yansanda suka gano a wani lamari na daban, har suka kama mutane biyu da ake zargi suna da alaka da al-Shabab.
Wadanda ake zargin kuma suna da alaka da kungiyar mayakan sakai ta al-Shabab dake Somaliya.
Sojojin Kenya da na Somaliya a garin Tabda, kasar SomaliyaSojojin Kenya da na Somaliya a garin Tabda, kasar Somaliya
x
Sojojin Kenya da na Somaliya a garin Tabda, kasar Somaliya
Sojojin Kenya da na Somaliya a garin Tabda, kasar Somaliya

Jiya lahadi,’Yan Sanda suka ce sun kai somamen ne da safiyar lahadi a wani gida dake wajajen fitar birnin Mombasa,a birnin ne babbar tashar jiragen ruwan kasar take.

Jami’ai suka ce an kashe daya daga cikin  mutanen a cikin gidan, yayinda na biyun kuma, ya gamu da ajalinsa lokacinda yake kokarin gudu.

Wannan somamen shine na baya bayan nan, a fito na fito da ake tayi tsakanin ‘Yan Sanda, da masu kishin addini, da ‘yan aware dake kan gabar teku a kasar.

Magoya bayan al-Shabab sun sha kai hare hare domin nuna adawarsu da shawarar da Kenya ta yanke na tura sojoji zuwa Somalia, domin su yaki mayakan sakai masu zazzafar ra’ayi.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti