Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yanzu Haka Ana Rigima A Masar


庄园外观
庄园外观

Anyi taho mu gamu a tsakanin masu zanga-zanga a biranen Alkahira da Alexandria, lokacin da dubban masu zanga-zanga suka cika tituna domin nuna goyon baya ga shugabannin soja da kuma masu goyon baya ga kungiyar Muslim Brotherhood.

A birnin Alexandria,magoya baya da wadanda basa goyon bayan hambararen shugaba Mohammed Morsi sun jejjefi junansu da duwatsu kowane bangare yana yiwa dayan (Tofin Allah Tsine).

A birnin Alkahira kuma, Magoya bayan Morsi sun gwabza fada da dubban masu zanga-zangar amsa kiran shugabbanin soja da su fito su hadu domin fara zanga-zanga a Dandalin Tahrir.

Jagoran rundunar sojin Misra Abdel Fattah el-sissi yace wajibi ne a fito ayi zanga-zangar nunawa matakan da soja ke dauka goyon baya domin karfafa gwiwar yaki da ayyukan ta’addanci.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG