Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yarjejeniyar Amurka Da Jami'ar ESCAE a Kasar Nijer.


 Yarjejeniyar Amurka Da Jami'ar ESCAE
Yarjejeniyar Amurka Da Jami'ar ESCAE

Cibiyar raya al’adun AMURKA a jamhuriyar NIJER ta cimma wata yarjejeniyar aiki tsakaninta da wata jami’a mai zaman kanta dake birnin yamai. Jakadiyar amurka a nijer ambasada Eunice Reddick ce ta saka hannu a wannan yarjejeniya da sunan gwamnatin amurka.

Wakilin muryar amurka sule mumini barma na dauke da karin bayani a cikin wannan rahoto.

A karkashin wannan yarjejeniya sashen bada horo a fannin turancin ingilishi wato the english language programm na cibiyar raya al’adun amurka a nijer zai koma karkashin makarantar ESCAE bayan shekaru 35 na aikin karantar da jama’a. a kalla mutun 1000 ‘yan asalin kasashe 18 mazauna kasar nijer masu sha’awar koyon turancin inglishin amurka ne ke rejistar sunayensu a cibiyar raya al’adun amurka a kowane wata ukku . A cewar malan idi barau jami’in hulda da ‘yan jarida a ofishin jakadancin amurka bayan dogon bincike ne gwamnatin amurka ta amince da wannan sauyi sakamakon yarda da sahihancin wannan makaranta ta escae.

Babban darektan makarantar ESCAE victor akessi ya tabbatarwa jakadiyar amurka a nijer cewa makarantarsa zata yi dukkan iya abinda ya dace domin kare darajar da aka san wannan sashen horo na cibiyar raya al’adun amurka da ita shekaru aruru.

An dai saka hannu akan wannan yarjejeniya a gaban babban magatakardan ofishin ministan ilimi mai zurfi dake wakiltar gwamnatin jamhuriyar nijer a wannan buki. Idan ALLAH ya kaimu ranar 1 ga watan oktoba ne za a soma bayerda horo a wannan sabon sashe na english language programm wanne jakadiyar amurka ambasada eunice reddick tace tun a 2003 aka riga aka mika harakokin tafiyarda makamantansa na kasashen yammacin africa ga makarantu masu zaman kansu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00


XS
SM
MD
LG