Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Wasu Kasashe 11 Basu Cimma Yarjejeniyar Cinikayya Ta TPP Ba


Wakilai a taron yarjejeniyar cinikayya da ake kira TPP a takaice.
Wakilai a taron yarjejeniyar cinikayya da ake kira TPP a takaice.

A daren jiya ne babban jami'in cinikayya na Amurka Michael Froman ya bayyana haka a wani taron manema labarai

Yanzu dai an kammala shawarwari da nufin kulla yarjejeniyar cinikayya tsakanin Amurka da wasu kasashe 11, amma ba'a cimma daidaito ba.

A wani taro da manema labara a daren jiya Jumma'a, babban jami'in Amurka kan harkokin cinikayya kuma wakilinta a taron, Michael Froman, yace kasashe 12 da suke gudanar da shawarwarin sun samu muhimmin ci gaba, har suna da kwarin guiwar cewa yanzu fiye da ako wani lokaci an kusa cimma matsaya.

An kwashe shekaru ana gudanar da shawarwari domin kulla yarjejeniyar cinikaya da ake kira TPP, har ana zaton an kusa kammala shawarwarin. A wannan mako, ministocin harkokin cinikayya na ksashen da shirin ya shafa, sun hallara a Hawa'ii domin ci gaba da shawarwarin.

Yarjejiniyar TPP idan har aka kulla zata shafi kusan kashi 40 cikin dari na tattalin arzikin duniya.
Batutuwan suna da sarkakiya ta fuskar siyasa, da suka hada da kyale a yi karin jigilar shinkafa zuw a Japan, karin shigar da sukari zuwa Amurka, kara bude kasuwar albarkatun daga dabbobi kamar su madara a Canada,da kuma kara fadada izini da iko kan magunguna da ake tsammanin zasu yi tasiri na tsawon shekaru 12.
Yarjejeniyoyin da aka kulla kan cinikayya a baya, sun fi maida hankali ne wajen rage kudin fito, da zummar sa kayayyaki su yi arha.

Masu goyon bayan yarjejeniyar TPP sun ce wannan yarjejeniyar zata daidaita bakin dokokin tsakanin kasashenn da suke cikin shirin, domin saukaka cinikayya da mu'amala a fadin duniya.

Wani Lauya Tim Brightbill, wanda ya kware wajen shari'ar harkoki cinikayya, yace kyakkawar yarjejeniya zata kasance "babbar fa'ida" ga dukkan kasashe da suke cikin shirin. Duk da haka yayi gargadin cewa duk wani daidaito wanda ba zai taimakawa sashen kere-kere da sarrafa kayayyaki na Amurka, da samar da ayyukan yi, ba zai sami amincewa daga majalisun dokokin Amurka ba.

XS
SM
MD
LG