Asabar, Fabrairu 13, 2016 Karfe 16:10

  Labarai / Sauran Duniya

  Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Isra'ila Da Hamas Ta Fara Aiki

  Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton da takwaranta na kasar Misra Mohammed Kamel Amr,
  Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton da takwaranta na kasar Misra Mohammed Kamel Amr,

  Yarjejeniyar tsagaita wuta  tsakanin Isra’ila da Gaza da aka cimma karkashin jagorancin kasar Misra ta fara aiki a daren jiya Laraba, sai dai kafin nan saida aka sake yin musayar wuta tsakanin dakarun Isra’ila da mayakan Hamas dake jagorantar garin na Palasdinawa.

  Mutanen garin Gaza sun shiga tituna suna murna. An ji karar bindiga da aka rika harbawa a iska na nuna farinciki.

  Ministan harkokin kasashen ketare Mohammed Kamel Amr ne ya sanar da yarjejeniyar a birnin Alkahira Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton kusa da shi, kasa da sa’oi biyu kafin karfe tara na dare agogon kasar lokacin da wa’adin tsagaita wutan da aka debar masu zai cika.

  Sharuddan tsagaita wutan sun hada da sassan biyu su daina kai hare hare, a kuma bude kan iyakar Gaza domin safarar kaya da kuma walwalar jama’a. Za a bada damar sa’oi 24 na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar. Misira zata sa ido kan sassan biyu domin ganin an aiwatar da yarjejeniyar.

  An cimma matsayar ne sa’oi bayan gagarumin yunkurin diplomasiya da ya
  Hada da Clinton, da kuma Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon.

  Clinton ta bayyana yarjejeniyar a matsayin “wani lokaci mai muhimmanci a yankin.” Ta kuma yabawa sabuwar gwamnatin kasar Misira domin taka muhimmiyar rawa a wannan yunkurin da kuma alkawarin da gwamnatin tayi na hada hannu da Washington wajen ganin cewa an kiyaye yarjejeniyar.

  Da yake magana a birnin Alkahira, shugaban kungiyar Hamas Khaled Meshaal yace Isra’ila ta amince da sharudan Hamas na yarjejeniyar. Ya bayyana hare haren sararin sama da Isra’ila ta kai a matsayin wani “hakar” da bata cimma ruwa ba.

  A birnin Kudus, Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya godewa Clinton da shugaban Amurka Barack Obama sabili da yunkurinsu ya kuma ce Isra’ila zata nemi ganin an sami zaman lafiya mai dorewa tare kuma da ci gaba da daina musayar wuta.

  Ministan tsaron kasar Isra’ila Ehud Barak ya kuma ce, Isra’ila ta cimma galibin gurorinta, ta lalata rokoki da kai hari a mafakar Hamas. Ya kuma bayyana cewa, makaman kakkabo harsasai masu linzaminta sun kakkabo sama da rokoki 500 da aka harba zuwa cikin kasar daga zirin Gaza.

  Sanarwar da fadar White House ta bayar tace shugaba Obama ya yabawa Firai Ministan Isra’ila “yayinda ta jadada cewa Isra’ila tana da ‘yancin kare kanta.”

  Sauti

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye