Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yin Tafiya Kadan Na Kauda Hatsarin Kamuwa Da Ciwon Suga


Wani abun gwajin ciwon suga a jiki
Wani abun gwajin ciwon suga a jiki

Wani bincike daga Jami’ar George Washington ya bayyana cewa, yin tafiya ta minti 15 bayan cin abinci yana hana tsofaffi kamuwa daga kashi na biyu na ciwon suga

Wani bincike daga Jami’ar George Washington ya bayyana cewa, yin tafiya ta minti 15 bayan cin abinci yana hana tsofaffi kamuwa daga kashi na biyu na ciwon suga. Wannan yana rage yawan sikarin cikin jini, kuma tafiya mai dan nisa ita ma na kara raguwarsa.

Karuwar yawan siga cikin jini bayan cin abinci, zata iya kara kashi na biyu na ciwon suga, don haka “hutawa bayan cin abinci abu mai hatsari ne”. Daya daga cikin masu bincike a kasar Amurka, Loretta DiPietro, tace binciken da suka yi na farko ya nuna, wasanni bayan cin abinci na rage hatsarin, domin bayan abinci sikarin cikin jini na karuwa sosai.

Binciken ya gano cewa tafiya ta minti 15 sau uku na da ingancin rage sugar cikin jini bisan sa’a 24 na tafiyar minti 45 ta rage yawan sigar jinin. Amma tafiyar minti 15 bayan cin abinci tafi inganci sosai wajen rage yawan sikarin jini bayan cin abinci, musamman wannan yafi ga tsaffin mutane.

Mai binciken tace, tsofaffin mutane na da hatsarin rage sigar jini bayan cin abinci, saboda matsalar abinda ke kara yawan sikari ko rage shi daga jikinsu.
Sun kuma gano cewa, lokacin yin wannan tafiya, mafi kyau shine bayan cin abincin yamma, wanda shine yafi yawa daga cikin abincin yini. Don haka yana kara yawan suga cikin jini.

Binciken ya gano, karuwar ta suga na “dadewa cikin dare zuwa safiya”, amma tana raguwa sosai yayinda mutane suka fara tafiya bayan cin abinci.
Masu binciken sun binciki tsofaffi 10 ‘yan shekara 60 da kuma fiye, wadanda ke cikin hatsarin kamuwa da kashi na biyu na ciwon suga, domin karuwar yawan siga cikin jini bayan cin abinci domin rashin isashshen wasannin motsa jiki. Dr. DiPietro tace, wannan binciken zai rage matsalar kauda kashi na biyu na ciwon suga.

Rage nauyin jiki da wasannin motsa jiki sun tabbata mabudin kiyaye kashi na biyu na ciwon suga, wannan na faruwa yayinda jiki ke rage yawan sikarin jini.

Kungiyar ciwon suga ta Amurka tace akwai kimanin Amurkawa miliyan bakwai dake cikin hatsarin kamuwa da kashi na biyu na ciwon suga.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG