Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 'Yan Majalisar Indonesia ya Jawo Faduwar Hannayen Jari


Masu goyon bayan 'yar tsohon shugaban kasar Suharto
Masu goyon bayan 'yar tsohon shugaban kasar Suharto

A kasar Indoonesia zaben 'yan majalisar dokokin kasar ya haddasa faduwar hannayen jari.

A can kasar Indonesia kuma, hanayen jari ne suka fadi da wajen kashi uku daga cikin dari a jiya Alhamis, bayan da aka yi zaben wakilan Majalisar dokokin kasar, zaben da babar jam'iyar masu hamaiya bata tabuka abun kirki ba.

Sakamakon da aka gabatar ba'a hukunce ba, ya nuna cewa jam'iyar Democratic of Struggle ko kuma PDI-P a takaice, tana bukatar kafa gwamnatin kawance bayan data lashe kusan kashi ashirin daga cikin dari na kuri'un da aka kada a ranar Laraba.

Tilas jam'iyu su samu kashi ashirin da biyar na kuri'un da aka kada, ko kuma su lashe kujeru ashirin na Majalisar dokoki kafin su iya zaben wanda zai yi musa takarar shugaba a zaben da za'a yi a watan Yuli.

Duk da haka, ana sa ran dan takarar jam'iyar PDI-P, gwamnan birnin Jakarta, Joko Widodo shine zai shugaban kasa na gaba. Yace a shirye yake a kula yarjejeniyar raba mukamai.

To amma yawancin kamfanoni masu zabu jarurruka a kasar, sun baiyana tsoron cewa yarjejeniyar daunin iko zata dagula sauye sauyen da ake yiwa tattalin arzikin kasar, da suke ganin ana bukata domin bunkasa tattalin arziki mafi girma a yankin kudu maso gabashin Asiya.
Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG