Jami'an Tsaro A Bauchi Sun Kwato Jamila al-Mustapha
Jami'an tsaro na hukumar tsaron kasa ta SSS a Bauchi sun kwato wata karamar yarinya mai suna Jamila al-Mustapha wadda aka sace a kan hanyarta ta zuwa makaranta makonni biyu da suka shige

1
Jamila al-Mustapha sanye da rigarta ta makaranta da kuma jakar makarantarta, ranar alhamis 18 Nuwamba 2010 a ofishin Hukumar Tsaron kasa ta Najeriya, SSS, dake Bauchi a bayan da aka kwato ta daga hannun mutanen da ake zargin sun sace ta makonni biyu kafin

2
Jamila al-Mustapha tare da mahaifiyarta a ofishin hukumar tsaron kasa ta Najeriya, SSS, dake Bauchi a bayan da jami'an tsaro suka kwato ta daga hannun mutanen da ake zargin sun sace ta

3
Jamila A. al-Mustapha tare da mahaifinta, Barrister Ahmed al-Mustapha, tsohon rajista-janar na Hukumar Rajistar Kamfanoni da Kungiyoyi Masu Zaman Kansu ta Najeriya, CAC, bayan da jami'an tsaro suka kwato ta daga hannun wadanda ake zargi da sace ta.

4
Jamila al-Mustapha tare da iyayenta a ofishin hukumar tsaro ta kasa, SSS, a Bauchi, bayan da aka kwato ta a daren alhamis, 18 Nuwamba 2010 daga hannun wadanda suka sace ta makonni biyu kafin nan.