Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Matar Mataimkin Shugaban Nigeria, Hajiya Amina Namadi Sambo Zuwa Gidan Rediyon Muryar Amurka na VOA a Washington, DC, ran 20 ga Watan Oktoba, 2010

Gidan Rediyon Muryar Amurka (VOA) ya karbi bakuncin matar Mataimakin Shugaban Nigeria, Hajiya Namadi Sambo wacce tayo jagorancin mata da dama da suka hada harda matan wasu gwamnonin Nigeria. A lokacin ziyarar, Hajiya Amina da tawaggarta sun gana da babban shugaban gidan Rediyon na VOA, Mr. Dan Austin da mukarrabansa kamar su John Lennon da Negussie Mengesha. Haka kuma bakin sun tauuana da jagabannin gudanarda shirye-shiryen kiyon lafiya na USAID irinsu Joan Mower da Brian Armstead inda suka zanta akan hanyoyin hadin kai ta fannin gudanarda tarukkan wayarda kan jama'a, musamman mata, a jihohin Nigeria daban-daban. Wadanda suka rako Hajiya Amina Sambo a ziyarar sun hada da Hajiya Jummai Babangida matar gwamnan jihar Neja da Malama Yemesi Suswam, matar gwamnan jihar Benue da Hajiya Zainab Maina, tsohuwar shugaban Gamayyar Kungiyoyin Matan Nigeria (NCWS) ta Nigeria da sauransu. A lokacin ziyarar, Sashen Hausa na VOA yayi hira da Hajiya Amina Namadi Sambo inda tayi magana kan aiyukkanta na kiyon lafiya da sauran al'amurran da suka danganci mata da yara a Nigeria. Haka kuma an zagaya da bakin don nuna musu sassa daban-daban na VOA kamar dakunan watsa labarai da inda ake tsara shirye-shirye da fannonin injuna da sauransu.


Domin Kari

XS
SM
MD
LG