Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarukkan wayar da kan jama'a gameda cutar Kolera da aka yi a Gombe da Bauchi, a Nigeria

Sashen Hausa na Muryar Amurka yaci gaba da shirya tarukkan da ya saba wajen wayarda kan jama'a kan sanadi da kuma hanyoyin yin garkuwa da kamuwa da cutar kolera. daruruwan mutane ne suka halarci wadanan tarukkan na baya-bayan nan da aka shirya a jihohin Gombe da Bauchi dake arewancin Nigeria. daruruwan mutanen da basu sami mazaunin a cikin zauren atron ba, an zaunar da su a cikin wata rumfar da aka girka a waje. Jami'an da suka hada na VOA, gwamnati da masana duk sun nuna misalan hanyoyin da za'a bi a tsarkake ruwa, wanke hannye da sauran hanyoyin tsabtace na kariyar lafiya. Mutane fiyeda 800 suka rasa rayukkansu a cikin wannan bala'in na kolera da aka dade ba'a ga irinsa ba a tarihin Nigeria.


Domin Kari

XS
SM
MD
LG