Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarukkan inganta kiyon lafiya na gidan rediyon murkyar Amurka (VOA) a biranen kaduna da minna na Nigeria

A ci gaba da kokarinta na wayarda kan jama'a kan hanyoyin tabattarda lafiyarsu da ta iyalansu, Sashen Hausa na gidan rediyon Muryar Amurka, VOA, ta sake shirya wasu manyan tarukkan karawa juna ilmi a jihohin Neja da Kaduna dake arewancin Nigeria a cikin watan Disambar 2010. A tarukkan da aka gudanr a biranen Minna da Kaduna, dubban mutane ne suka halarta. A Kaduna, inda kamar mutane dubu hudu suka cika dakin taron, muhimman mutanen da suka halcri zaman sun hada da matar mataimakin shugaban Nigeria Hajiya Amina Namadi-Sambo da gwamnan jihar Kaduna Ibrahim Yakowa da kuma ministan lafiya na Nigeria. A Minna ma an sami halartar manyan bakin da suka hada da matar gwamnan jihar Neja, Hajiya Jummai Babangida Aliyu, da mataimakin gwamnan jihar da kwamishinan alfiya da sauran kusoshin gwamnati. Yayinda a Kaduna aka tinkari maganar lafiyar mata da 'yayansu, a Minna an dubi hanyoyin yaki da cutar cizon sauro ta Malaria ne. Kuma a dukkan biranen biyu, masana da jami'ai sun bada bayanai na irin barnar da cuttukka suke yi da hanyoyin garkuwa daga kamuwa da su. Mahalarta maza da mata kuma, wadanda suka yabawa VOA kan shirya tarukkan, har ila yau sunyi magana gameda matakan da suke dauka na samun ilmantuwa kan hanyoyin rigakafi da kuma kare kansu da iyalinsu daga kamuwa da wadanan cututtukkan na zamani. Muryar Amurka, VOA, tana shirya irin wadanan tarukkan ne tareda hadin gwaiwar Cibiyar Raya Kasashen Duniya ta Amurka (USAID).


Domin Kari

XS
SM
MD
LG