Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kai harin kunar bakin wake a Jalingo jihar Taraba ne da niyyar kashi kwamishinan 'yan sandan jihar Taraba, Mamman Sule

'Yan kallo sun yi cincirindo a wurin da aka kai harin kunar bakin wake na Bom kan babban Titin birnin Jalingo, Nigeria ran litinin 30, ga watan Afrilun shekarar 2012. A lokacin da wani dan harin kunar bakin wake a kan Babur ya nemi kutsawa ta cikin kwambar motocin dake dauke da Kwamishinan 'yan sandan jihar Taraba, Mamman Sule, inda ya tada boma-boman dake jikin babur din da yake kai a kan hanyar zuwa ofishin hukumar 'yan sanda dake kusa da ofishin Gwamnan jihar taraba dake Jalingo.


Domin Kari

XS
SM
MD
LG