Accessibility links

A Kenya ana Ci Gaba Da Ayyukan Ceton Jiragen Sojan Uganda.


A wan nan hoto da rundunar mayakan Kenya ta bayar ana nuna ceton matukin jirgin Uganda da yayi hadari.

Masu aikin ceto a Kenya suna ci gaba da kokarin kaiwa ga inda jiragen soja masu saukar ungulu na kasar Uganda suka yi hadari

Masu aikin ceto a Kenya suna ci gaba da kokarin kaiwa ga inda jiragen soja masu saukar ungulu na kasar Uganda suka yi hadari a kan dutsen Kenye dake tsakiyar kasar.
Jami’an rundunar sojojin Kenya sun fada yau talata cewa sun hango inda baraguzan jiragen suke daga sama, amma basu san makomar wadanda suke jiragen ba ahalin yanzu.
A wan nan hoto daga hanun dama sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ce da shugaban kasar kenya Mwai Kibaki.
A wan nan hoto daga hanun dama sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ce da shugaban kasar kenya Mwai Kibaki.

Ranar litinin masu aikin ceto sun gano jirgi na ukun, wadda yayi saukar gaggawa kan dutsen na Kenya. An ceto duka mutane bakwai da suke cikin wan nan jirgin.
Jami’an Kenya suka ce masu bincike suna aza laifin hadarin kan munin yanayi.
Tun litinin ake samun rahotanni masu sabani da juna kan makomar jiragen. Rahotannin farko sun nuna cewa an gano duka jiragen uku, kuma tuni har wai an ceto duka jami’ai dake cikin jirgin.
Jiragen yakin sojan Ugandan masu saukar ungulu, suna kan hanyar zuwa Somalia ne domin kara karfi ga rundunar da tarayyar Afirka ta tura kasar, domin ayyukan kiyaye zaman lafiya.
Jirgi na hudu ya sauka lafiya a wani sansanin soja dake arewa maso gabashin Kenya.
XS
SM
MD
LG