Accessibility links

PM Habasha ko Ethiopia Meles Zenawi Ya Rasu.


Marigayi PM Ethiopia Meles Zenawi

A wunin Talatan nan ne tashar talabijin ta kasar ta bada sanarwar mutuwarsa, tana cewa ya fara murmurewa daga jinyarda yake yi a kasashen waje.

PM Meles Zenawi ya juma yana fama da wata larura da ba a bayyana irin cutar ba, kuma fiyeda wata guda ba a ganshi a bainar jama'a ba.
Marigayi Zenawi da uwargidansa.
Marigayi Zenawi da uwargidansa.

Marigayi Zenawi yayi mulkin kasar na fiyed a shekaru ashirin, bayanda gamayyar kungiyoyin 'yan tawaye da yake yiwa jagoranci da ake kira Ethiopian Peoples's Revolutionary Democratic Front, ko EPRDF a takaice suka kwace iko a kasar a 1991.

Kasashen duniya sun yabawa shugaban kasar mai rasuwa saboda ci gaba da kasar ta samu a fannin tattalin arziki, da ilmi, da kuma kiwon lafiya. Amma kungiyoyin kare hakkin Bil-Adama suna matukar sukarsa kan cin zarafin Bil-Adama daban daban, ciki harda hana kafofin yada labarai masu zaman kansu walwala.

Karkashin mulkinsa hulda da kasashen waje sun hada harda zaman dar dar da Eritrea. kasashen biyu sun gwabza fada saboda rikicin kan iyaka daga 1998 zuwa shekara ta 2000, yakin ya halaka akalla mutane dubu 70,000.

Haka kuma ana kallon gwamnatinsa a matsayin kawar Amurka a yaki da take yi kan ta'addanci,kan haka ne Habashan ta tura sojoji zuwa Somalia domin ta yaki mayakan sakai masu da'awar islama.
XS
SM
MD
LG