Accessibility links

'Yan Zanga Zanga A Kenya Sun Kashe Dansanda Daya A Wani Hari Da Gurneti.


Gungun matasa musulmi suke cicirindo kusa da tayoyi da suke konewa, a zanga zangarda ta biyo bayan kisan wani malamin addinin Musulunci.
‘Yansanda sun ce an kashe wani dansanda daya a wani harin gurneti da masu zanga zangar suka kai musu. Tunda farko a wunin talatan, sai da ‘yansanda suka harba hayaki mai sa hawaye a kokarin tarwatsa masu zanga zanga dake jifar su da duwatsu.
Aboud Rogo Mohammed, malaminda aka kashe a bayyanarsa gaban kotu lokacin yana raye.
Aboud Rogo Mohammed, malaminda aka kashe a bayyanarsa gaban kotu lokacin yana raye.

Mazauna birnin na Mombasa sun ce sai da suka nemi mafaka yayainda matasa musulmi suke hatsaniya kan tituna. Wakilin Muriyar Amurka na Sashen Swahili, yace matasan sun farfasa kantuna suna diban ganima, kuma sun kona majami’u biyu a wunin talatan nan.
Malaman addinin islama suna kira da jama’a su kai zuciya nesa.

Wani malami dake tareda majalisar limamai da da masu wa’azi a Kenya, Mohammed Khalifa, yace “an kashe wasu mutane da basu san hawa ba balle sauka, wasu kuma an jikkata su” muna so a dawo da zaman lafiya a Mombasa”.

Zanga-zangar ta barke ne bayanda wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, suka bude wuta suka kashe Aboud Rogo Mohammed, mutuminda Amurka, da Majalisar Dinkin Duniya suke zargi da taimakawa mayakan sakai na al-shabab a Somalia.
XS
SM
MD
LG