Accessibility links

Wani Ba-Amurke Ya Lashe Tambolar Dala Milyan 337

  • Aliyu Imam

Wani kanti yake tallar tambola mai tsoka a jihar New Jersey.
Jumma’a, wani dan shekaru 44 da haifuwa, a jihar Michigan dake arewacin Amurka, ya gabatar da kansa a matsayin mutuminda ya lashe tambola mafi tsoka na uku a duk tarihin tambolar da ake kira Powerball.

Donald Lawson wadda yake aikin injiniya na jiragen kasa, yayi ritaya, bayanda ya tabbatar cewa shine ya sami nasarar cin tambolar na dalar Amurka milyan 337. Saboda hakama ya sa wasu daga ‘yan uwansa suma suka yi ritaya domin yana son ya raba arzikin tareda su.

Lawson ya tsaida shawarar karbar dala milyan 158.7 lokaci daya, maimakon jira shekara da shekaru domin ya karbi kudaden baki dayansu watau dala milyan 337 kamin a cire haraji.

Lawson wanda ya shiga sahun masu arzikin milyan yace rayuwars a zata “inganta”, duk da haka yace yana shirin ci gaba da rayuwarsa a saukake, wadda yace zai hada da zuwa wurin cin abincin zamanin nan d a ake kira McDonalds.

Lawson ya sayi tikitin tambolar ne a wani gidan mai, kuma shi da kansa ya zabi lambobin shida, maimakon barin na’ura ta zaba masa.
XS
SM
MD
LG