Accessibility links

Farashin Kayan Abinci Ya Daidaita A Watan Agusta


Wani makeken allo a harabar Bankin Duniya,mai tattara bayanan mutane a fadin duniya masu fuskantar matsanancin 'yunwa.
Hukumar abinci da aikin gona ta Majalisar Dinkin Duniya mai cibiya a birnin Roma, tace alkalumanta kan farashin abinci, bai canza ba cikin watan nan. Hakan, hukumar taci gaba da cewa, ya sassauta tsoron da aka fara ji domin fari a bazarar bana da ya faru a Amurka, da gabashin turai, zai ci gaba da tura farashin kayan abinci gaba-gaba, yayinda farashin muhimmai kayan abinci, kamar masara, waken soya, da alkama suke kara bushewa domin karancin ruwa.
Sakewar yanayi yana iya sa a farashin abinci ya hauhawa a kasashe masu tasowa.
Sakewar yanayi yana iya sa a farashin abinci ya hauhawa a kasashe masu tasowa.

A cikin watan Yuli farashin kayan abinci ya haura da kamar kashi 6 cikin dari.
Darekta janar na hukumar Jose Graziano da Silva, yace rashin tashin faracin abinci cikin watan Agusta ya karfafa guiwa. Yace karin farashinda aka samu bai kai ace “duniya tana fuskantar tsadar abinci ba”.

Rahoton hukumar na watan Agustan, ya nuna farashin abinci dangin hatsi, mai da suka hada da kitse bai sake ainunba cikin watan jiya, amma farashin sukari yayi kasa sosai, sai dai farashin nama da dangin madara, wadannan farashinsu sun karu.

Kodashike farashin kayan abinci sun daidaita a duniya, duk da haka farashin
XS
SM
MD
LG