Accessibility links

Hukumar Harajin Amurka Ta Bada Tukuicin Dala MIlyan 104 Ga Wani Mai Tsegumi


Sakataren Baitul Malin Amurka Timothy Geithener, da ta harkokin waje Hillary Clinton.
Hukumar harajin Amurka ta bada tukuicin dala miliyan 104 ga wani tsohon ma’aikacin bankin UBS mai cibiya a kasar Switzerland bayan ya gaya ma ta yadda bankin ke taimakawa dubban Amurkawa su na gujewa biyan haraji ta hanyar yin amfani da bankunan ajiya a kasashen ketare.

Lauyoyin wanda ya yi tonon asirin, mai suna Bradley Birkenfeld, su ne su ka yi sanarwar cewa an ba shi tukuicin a jiya talata. Su ka ce wannan ne tukuici mafi tsoka da hukumar harajin Amurka, ta IRS ta taba bayarwa. Hukumar ta IRS ta tabbatar da cewa ta bayar da tukuicin.

Ana yabon Birkenfeld da gayawa jami’an Amurka yadda bankin na UBS ya taimaki Amurkawa attajirai su ka rika yin ajiya a wurin shi, kuma ya kula mu su da kadarorin su da aka kiyasta kan kudi dala miliyan dubu 20 kuma ya taimake su, su ka cuci gwamnatin Amurka.
XS
SM
MD
LG