Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Sudan da Sudan ta Kudu na Cigaba da Tattaunawa

Shugaba Omar al-Bashir na Sudan ta Arewawe takwaransa na Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaba Omar al-Bashir na Sudan ta Arewawe takwaransa na Sudan ta Kudu Salva Kiir

Shugabannin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu za su gana a rana ta biyu a yinkurinsu na cimma yarjajjeniya game da dadaddun matsalolin da su ka biyo bayan rabuwarsu a bara.

Shugabannin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu za su gana a rana ta biyu a yinkurinsu na cimma yarjajjeniya game da dadaddun matsalolin da su ka biyo bayan rabuwarsu a bara.

Za a cigaba da tattaunawar tsakanin Shugaba Omar al-Bashir na Sudan da Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ne a yau Litini a Addis Ababa babban birnin Habasha.

Wani mai magana da yawun bangaren Sudan Sudan ya ce bayan karon farko na tattaunawa a jiya Lahadi bangarorin biyu sun daidaita kan akasarin batutuwan tattalin arziki, man fetur da cinakayya, to amman har yanzu su na da sabanin ra’ayi game da batun tsaro.

Takaddamar da ta biyo bayan samun ‘yancin kan Sudan ta Kudu daga Sudan a cikin watan Yuli na 2011 ta hada da ikirarin da kowannensu ke yi na mallakar yankin Abyei mai arzikin mai.

Sudan na kuma zargin Kudu da taimakawa da kayan yaki ga ‘yan tawayen da ke yankuna biyu na kudun, a sa’ilinda ita kuma Sudan ta Kudun ke zargin dakarun Sudan da kai mata hare-haren bama-bamai.
XS
SM
MD
LG