Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kasashen Duniya Na Yin Taro a Bamako.


Babban Magatakardan MDD Ban Ki-moon ya na ganawa da Firai Ministan kasar Mali, Cheikh Modibo Diarra.

shugabannin kasashen duniya na neman hanyoyin shawo kan matsalar 'yan gwagwarmayar Islama masu alaka da al-Qaida a arewacin kasar Mali.

Shugabannin kasashen duniya za su yi wani zaman taro a yau Jumma’a a Bamako babban birnin kasar Mali domin su tattauna hanyoyin kawar da kungiyoyin ‘yan gwagwarmayar Islama masu alaka da al-Qaida, wadanda ke rike da arewacin kasar.
Taron na birnin Bamako zai hada da wakilan Majalisar Dinkin Duniya da na kungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS, da na kungiyar kasashen Afirka, da kuma na tarayyar Turai.

Kungiyar ECOWAS ta gabatar da shawarar tura wata runduna mai karfin sojoji dubu uku don ta kakkabe ‘yan gwagwarmayar na Islama amma ‘yan kasar Mali ba sa goyon bayan gudunmowar sojojin kasashen waje, sun gwammace su warware rikicin kasar su ta hanyar siyasa.

Juyin mulkin da aka yiwa shugaban kasar Mali a ranar ishirin da biyu ga watan Maris din da ya gabata ne ya jefa ta cikin halin hargagi da hargitsi. ‘Yan gwagwarmayar Islamar da su ka kama arewacin kasar sun aiwatar da hukunce-hukuncen kisa, da yanke gabobin jiki da kuma zanewa da bulala a wani kokarin neman karfafa ta su irin shari’ar Islama.

A makon jiya Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da wani kudirin share hanyar tura rundunar sojojin ta kasashen ECOWAS. Kudirin ya baiwa shugabannin kasashen Afirka wa’adin kwanaki 45, su tsara wani shirin yin amfani da karfin soja.

Kasar Faransa wadda ta yiwa Mali mulkin mallaka, ita ce ta jagoranci kiran daukan mataki a zauren Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, kuma ita ce ta gabatar da kudirin. Da yake magana a kasar Senegal a makon jiya, shugaba Francois Hollande, ya fada cewa ba za a iya jurewa abubuwan firgitarwar da ke faruwa a arewacin kasar Mali ba.

Jerin gwanon da daruruwan mutane ke yi a ‘yan kwanakin nan a Bamako, na kara fito da bambancin ra’ayin jama’a a fili, wasu na so a gaggauta kai gudunmowar sojojin kasashen waje, a yayin da wasun su kuma, su ka dage da duk karfin su, ba sa goyon baya.
XS
SM
MD
LG