Accessibility links

An Bankado Shirin Neman Kaiwa Jam'iyar ANC Hari

  • Halima Djimrao-Kane

Shugaba Jacob Zuma na rera waka ranar bude babban taron jam'iyar ANC a Bloemfontein, a kasar Afirka ta Kudu.

'Yan sandan kasar Afirka ta Kudu sun kama wasu mutane hudu masu tsattsauran ra'ayi bisa zargin shirya makarkashiyar kai hari kan babban taron ANC

‘Yan sandan kasar Afirka ta Kudu sun kama wasu masu tsattsauran ra’ayi hudu wadanda ake zargi da shirya makarkashiyar kai hari a lokacin da jam’iyar da ke mulkin kasar ke gudanar da babban taron ta.

A yau litinin hukumar ‘yan sandan kasar ta bayar da sanarwar kama mutanen , amma ba ta yi cikakken bayani ba, ta ce ranar lahadi aka kama mutanen ‘yan shekaru 40 zuwa 50.
Jam’iyar ANC ce ke rike da mulkin kasar Afirka ta Kudu tun shekarar 1994 da aka kawo karshen mulkin turawan kasar ‘yan tsiraru, kuma ta na yin babban taron ta na kwanaki biyar a birnin Bloemfontein.

Kakakin ANC, Keith Khoza, ya fada a yau litinin cewa har yanzu jam’iyar na jiran cikakken rahoto a kan kama mutanen, kuma ya ce makarkashiyar kai harin wani al’amari ne mai tayar da hankali. Ya ce barazanar da ake yi saboda launin fata, abu ne mai ban tsoro, amma ya ce jam’iyar ANC za ta ci gaba da yin babban taron ta cikin gagarumin tsaro.

Ya ce sun damu saboda har yanzu a cikin su akwai wasu daidaikun mutanen da ke da irin wannan tunani. Ya ce hakan ya na nufin cewa ana fuskantar babban kalubale. Ya ce kasar Afirka ta Kudu ta ga abu mafi muni, kuma ya ce ba sa fatan sake komawa cikin yanayin tashin hankali saboda launin fata ko ta’addanci. Ya ce hakan bai dace da abun da ‘yan kasar Afirka ta Kudu baki dayan su ke kokarin cimma ba.

Jam’iyar Federal Freedom ta gwagwarmayar kwatar ‘yancin turawan Afrikaner ‘yan tsiraru, ta bayar da sanarwar cewa biyu daga cikin wadanda aka kama mambobin ta, amma ta nisanta kan ta da duk wata makarkashiyar shirya kai hari.
XS
SM
MD
LG