Accessibility links

Dalibar Da Aka Yi Ma Fyade A Indiya Ta Mutu


Indiyawa da suka taru su na addu'a ma dalibar da wasu mutane suka taru suka yi mata fyade, wadda ta rasu yau asabar

'Yan sanda sun damke mutane 6 da ake tuhuma, kuma bayan tuhumar fyade, a yanzu zasu fuskanci tuhumar kisan kai da yake dalibar ta rasu

Wata dalibar kasar Indiya wadda wasu mutane suka taru suka yi mata fyaden taron dangi a wannan wata cikin wata motar safa a New Delhi, ta rasu yau asabar da asuba a wani asibitin kasar Singapore.

Wata sanarwar da asibitin Mount Elizabeth ya bayar, ta ce wannan mace mai shekaru 23 da haihuwa ta rasu cikin "kwanciyar hankali" da asuba.

Firayim minista Manmohan Singh na Indiya yace yayi matukar bakin cikin mutuwar wannan matashiya. Yace kowa yana iya fahimtar irin fusatar da al’ummar kasar Indiya ke nunawa kan lamarin wannan daliba.

A yau asabar aka shirya za a mayar da gawarta zuwa kasar Indiya.

An fuskanci zanga-zanga da gangamin dubban jama’a a birnin New Delhi tun ranar da aka kai ma wannan mace farmaki. Jami’ai a birnin New Delhi sun ce su na damarar ganin karin zanga-zanga a bayan mutuwarta yau asabar.

An ce wannan mace tana tafiya tare da wani abokinta namiji cikin wata motar safa ranar 16 ga watan Disamba a New Delhi sai wasu mazaje su 6 dake cikin motar suka ciro rodi na karfe suka lakkada musu duka da ita da wannan aboki nata. Daga nan suka yi ta yi mata fyade. Daga nan kuma sai suka jefa ta waje daga cikin motar tare da shi abokin nata.

‘Yan sanda sun damke mutanen shida da ake zargi da wannan danyen aiki, kuma an tuhume su da fyade. Yanzu kuma su na fuskantar laifin kisan kai a bayan mutuwarta.
XS
SM
MD
LG