Accessibility links

VOA 60 Afirka - Junairu 07, 2013


Wasu ‘yan bindiga sun kashe wasu mutane goma ta harbin su ko sarar su a wani sumame da suka kai kauyukkan jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeria. A Africa ta Kudu, tsohon shugaban kasa Nelson Madela na kara samu lafiya, bayan cutar hunhu da ya fuskanta a makonnin da suka wuce.‘Yan tawaye sun kame garin Alindao dake kudancin janhuriyar Africa ta Tsakiya. A Libya, Ministan cikin gida Ashour Shuail ya amince cewa makamai daga Libya sun jawo karin rashin zaman lafiya a yankin gabashin nahiyar Africa, sannan ya goyi bayan saka mayakan sa kai cikin rundunar ‘yan sanda.A kasar Ghana, mutane na bikin rantsar da sabon shugaba, duk da cewa masu adawa sunki hallartan taron rantsar da shugaban kasar.

XS
SM
MD
LG