Accessibility links

VOA 60 Afirka - Junairu 08, 2013


Yayin da ‘yan tawaye ke kara kusantar babban birnin Janhuriyar Afrika ta Tsakiya, shugaban kasar ya isa Brazzaville domin tattauna rigimar da shugaba Sassou-Nguesso.A kasar Cote ‘d Voire, shugaban asusun lamini na kasa da kasa Christine Lagarde yace rigima da makamai ne babban kalubalen cigaban Afrika a wani taro da ya hallarta a birnin Abidjan. Sabon shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama yayi Alkawarin hada kan kasa a bikin rantsar da shi. A Sudan kuwa, karo mai zaki na kara daraja a kasuwannin kasashen waje. A kayace mutan kasar Nijar suke, a fitowarsu ta biyu domin buga kofin kwallon kafa na nahiyar Africa da za’a fara a Afrika ta Kudu nan bada jimawa ba.

XS
SM
MD
LG