Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Kwana Uku Kenan A Rikicin Garkuwa Da Mutane A Algeria


Hoton masana'antar iskar gas dake Algeria
Hoton masana'antar iskar gas dake Algeria
Rikicin wadanda ake garkuwa da su a wani ginin masana’antar sarafa iskar gas a kasar Algeria dake hamada ya shiga ya cika kwana uku a yau jumma’a, ba tare da sanin halin wadanda ake garkuwa dasu suke ciki ba.

Dakarun Algeria sun kutsa a ma’aikatar sarrafa gas din Ain Amenas jiya alhamis, inda suka kubutar da wasu ma’aikatan kasar waje da ba a san ko suwaye ba, amma wasu da yawa cikin wadanda aka sace da wadanda aka yi garkuwa da su kuma sun mutu.

Gwamnatocin kasashen waje, wadanda ba’a iya sanar dasu akan farmakin ba kafin a kai shi, suna kokarin tantance halin da mutane 41 wadanda ake garkuwa dasu suke ciki wadanda ke tsare a ginin.

Akalla wasu guda 4 da akayi garkuwa dasu, gwamnatin kasar ta tabbatar da da cewa suna nan lafiya kalau, 3 daga cikin su yan Japan ne daya daga cikin su kuma dan kasar Ireland ne. Sai dai halin da sauran ke ciki ne ba’a sani ba, wadanda suka hada da Amurkawa, ‘yan Japan, Norway, Romania, Philippins, Ingila, Faransa, Malaysia, da Australia.
XS
SM
MD
LG