Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Henry Okah Da Laifin Ta'addanci


Hoton Henry Okah kennan, dan Asalin Najeria wanda ake tuhuma da ta'adanci a kotun Afirka ta Kudu ran Junairu 21, 2013.
Hoton Henry Okah kennan, dan Asalin Najeria wanda ake tuhuma da ta'adanci a kotun Afirka ta Kudu ran Junairu 21, 2013.
Wata kotun Afirka ta Kudu ta samu wani dan Najeria da laifin ta’addanci ta shirya fashewar bom da yayi a shekara ta 2010 har mutane 12 suka mutu.

A yau litinin, kotun ta samu Henri Okah da laifuffuka guda 13 da suka danganci fashewar boma-bomai guda biyu a babban birnin Nijeria, Abuja a ranar da ake bikin samun ‘yan cin kai. Kotun bata fadi hukuncin da ta yanke wa Okah ba tukunna.

Jami’an tsaro sun tsare Okah a Afirka ta Kudu ne washegarin fashewar boma-boman. Yace shi babu hannunsa a cikin wannan hari.

Ana kuma tuhumar shi da shugabantar kungiyar ‘yan tsagera ta Naija Delta a takaice MEND, amma ya musanta wannan kazafi.

MEND dai, ta kaiwa masan’antun sarrafa danyen mai na Najeria hare-hare da dama, tana mai neman karin kaso daga arzikin da kasar ke samu daga yankin Niger Delta. Da yawa daga cikin ‘yan kungiyar sun ajje makamansu a shekata ta 2009, a karkashin wani shiri na afuwa da gwamnatin Najeria ta samar.
XS
SM
MD
LG