WASHINGTON, D.C -- Wani sabon nazari da akayi ya nuna cewa mutane da suka daina shan cigari kafin su kai shekaru 40, kan iya rayuwa har i zuwa shekarun wadanda basu taba shan cigari ba.
Manazarta a jami’ar Toronto sun bada rahoton cewa daina shan cigari kafin a cika shekaru 40 na dawo da shekaru guda 10 da shan cigarin ke yankewa rayuwar mutum.
Amma kuma hakan, ba yana nufin shan cigari bashi da wata matsala kafin a cika shekaru 40.
Shugaban wadanda suka yi wannan nazari Prabhat Jha, farfesa ne a jami’ar Toronto, kuma shine shugaban cibiyar nazarin lafiyar duniya ta asibitin St. Michael yace mutanen da suka taba shan cigari ka iya mutu kafin wadanda basu taba sha ba.