Accessibility links

Kungiyar Taurarin Kwallon Kafar Afirka Na 2013


Zabi zakarun gurza tamaula da kuke son gani cikin Kungiyar Kwallon Kafa ta Afirka ta 2013, kuma ta Muryar Amurka. Zabi ‘yan wasa 4, ta hanyar fitar da tauraro guda daga wadannan rukunoni 4 na Mai Tsaron Gida, Dan Wasan Tsakiya, Dan Wasan Gaba da Mai Tsaron Baya. Za a fara jefa kuri’a ran 19 Janairu, a rufe ran 10 Fabrairu. Za a bayyana ‘yan wasan da suka yi nasarar shiga cikin Kungiyar a ranar 11 Fabrairu. Ana iya jefa kuri’a ta kan Intanet, ko ta hanyar aiko da Text dauke da sunan ‘yan wasan da aka zaba zuwa ga +12026701867. YADDA ZA A ZABI GWANI: Matsa sunan dan wasan da kake so daga kowane rukuni guda a kasa, sai ka latsa inda aka rubuta “Zabi dan Wasa”, sai kuma a je sauran rukunonin a yi haka. Launin suna da kewayen duk gwanin da ka zaba, zai sauya ya koma kore. Idan ka gama zabo gwanayenka hudu, sai ka matsa inda aka rubuta “Jefa Kuri’a”. Shi ke nan!!!

XS
SM
MD
LG