Accessibility links

Hillary Clinton Ta Sauka Daga Mukaminta


Hillary Clinton a lokacin da is birnin New Delhi, Mayu 7, 2012.
Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton za ta sauka daga mukaminta yau jumma'a yayinda za'a rantsar da mai maye gurbinta John Kerry.

Clinton tayi shirin yin jawabi ga ma’aikatan ma’aikatar harkokin wajen Amurka da rana kafin ta sauka daga kujerarata.

A wani kebabben biki, za'a rantsar da Mr. Kerry a matsayin sakataren harakokin waje na na biyu a mulkin shugaba Obama.

A lokacin da ake zaman tattaunawa akan mukamin Mr. Kerry, tsohon dan majalisar dattawa daga jihar massachusettes, ya fada wa abokan aikin sa cewa, ya yi imanai Clinton ta yi aiki sosai ba tare da gazawa ba. A nata bangaren, Clinton ta ce zata doshi abu na gaba a rayuwarta.

Duk da cewa bata fito fili ta tabbatar da kudurin ta na fitowa zaben shugaba ba, akwai rade-radin cewa za ta tsaya takarar a shekarar 2016, kamar yadda ta yi a shekarar 2008, inda shugaba Obama ya lashe zaben a karkashin jam’iyyar Democratic.
XS
SM
MD
LG