Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Joe Biden Yayi Wa Iran Kashedi


Mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden da shugaban Jamus Angela Merkel.
Mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden da shugaban Jamus Angela Merkel.
Mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi wa Iran kashedi akan cewsa lokaci na kure mata na shiga shawarwarin diflomasiyya akan rikicin da ake yi na shirin nukiliyar ta.

Kalaman da Mr. Biden yayi, an buga su yau jumma’a a wata jaridar jamus inda yake ziyara da kuma halarta taron tsaro da za a yi a birnin Munich.

Mataimakin shugaban kasar Amurka ya ce, har yanzu akwai lokaci da kuma damar diflomasiyya tareda matsi akan tattalin arzikin Iran, amma ya nuna cewa wannan damar ba zata kasance ba har abada. Yace, mai yiyuwa ne a ci gaba da sa mata takunkumi da kuma karin matsin lamba daga kasashe.

A nata gefen, Iran na nuna alamar cigaba da nuna cewa ai shirinta na neman fasahar nukiliya na zaman lafiya ne, duk da cewa Amurka da sauran kawayenta suna tunanin cewa kudurin Tehran na yin makaman kare dangi ne.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG