Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Kafa Sabuwar Gwamnati A Tunisiya Ba Tare Da La'akari Da Siyasa Ba


Wani mutum na kuka a gaban hoton shugaban masu adawa a Tunisia, Chikri Belaid. REUTERS/Zoubeir Souissi
Firayim Ministan Tunisiya Hamadi Jebali ya ce zai kafa sabuwar gwamanati ba tare da la’akari da siyasa ba, sanadiyyar kisan gillar da aka yi wa wani fitaccen jagoran ‘yan adawa.

Mr. Jebali ya bayar da sanarwar wannan niyyar tasa ce a jiya Laraba ta gidan talabijin na kasa a daidai lokacin da dubban masu zanga-zanga ke ta arrangama da ‘yan sanda a babban birnin kasar sanadiyyar kisan gillar da ake yi wa Chokri Belaid, wani fitaccen jagoran gamayyar ‘yan son kowa sauyi da aka kafa bara. Yayin da arangamar ta kazance masu zanga-zanga sun cinna wuta ma hedikwatar jam’iyyar Islama ta Ennahda mai sassaucin ra’ayi. Wadda ke mulki a gwamnatin hadakar da ta kunshi wadanda ba ruwansu da manufofin addini.

Firayim Ministan yace sabuwar gwamnatin za ta kasance da takaitaccen sabon hurumin da ba zai wuce kula da kasar kawai ba kafin a yi zabe, kuma hakan zai faru da zaran an sami hali.

Belaid wanda shi ne shugaban jam’iyyar Popular Front, an bindige shi ne yayin da ya baro gidansa da ke birnin Tunis. Ba a dai kama kowa ba zuwa yanzu.

Bayan wasu ‘yan sa’o’i, jam’iyyar Popular Front ta bayar da sanarwar ficewa daga majalisar da aka kafa don rubuta sabon kundin mulkin kasa, kuma wani mai magana da yawun jam’iyyar ya gaya wa manema labarai cewa za su kira yajin aiki na kasa baki daya don nuna bacin rai kan kashe Belaid.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG